
A kwanakin baya, Mutane da dama a yankin Tudun Wanda da wasu unguwanni suna ta murna bayan tabbatar da mutuwar wani rikakken dan daba a Kaduna da ke Arewacin Najeriya.
Rahotanni daga Kaduna sun tabbatar da mutuwar sanannen ɗan daba abin da ya jawo martani daban-daban a yankin Wasu mazauna unguwar sun nuna farin ciki da mutuwarsa saboda zargin cin zarafi, da kisan kai dayiwa Wanda akalla sun kai kimanin Mutane 72.

Rahotanni daga jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar sanannen ɗan daba wanda ya addabi al’umma da dama. Majiyoyi sun bayyana cewa al’ummar yankin da dan daban ya fito sun nuna farin ciki kan lamarin da ya faru.
Rikakken dan daban, Abubakar Sadiq wanda aka fi sani da Habu Dan Damisa ya yi bankwana da duniya.
Wasu sun yi murna bayan mutuwar ‘dan daban Mutuwar matashin, ɗan unguwar Tudun Wada a Kaduna, ta faru ne ranar Laraba 27 ga watan Agustan 2025.
mutuwar ta jawo martani daban-daban tsakanin mazauna yankin Tudun Wanda da wasu unguwanni Yayin da wasu mazauna suka nuna farin ciki, suna murnar labarin rasuwarsa,
Saidai kuma bayan mutuwar Habu Dan-Damisa, sai hotonsa tareda da kakakin Majalisar jihar kaduna wato Yusuf Liman ya bayyana a kafafen yada labarai na zamani (social media), a inda Kakakin Majalisar ke zaune a motarsa tare da Dan Damisa, Wanda hakan ya kawo cece-kuce a tsakanin al’ummar kaduna.
Bugu da Kari, wasu na zargin cewa duk Ta”addancin da Dan Damisa ke tafkawa akwai masaniya da daurin gindi da yake samu ta bangaren Kakakin Majalisar jihar kaduna da wasu jiga-jigan ‘yan siyasar jihar.
Ana Kuma zargin shi Yusuf Liman da taimakawa Dan-Damisa wurin karbar shi a hannun hukuma duk lokacin da aka kamashi ko aka kaishi gidan yari, shiyasa yake con karensa ba babbaka.
Kafin hada wannan rahoto, an nemi jin ta bakin shi Yusuf Liman Kakakin Majalisar jihar kaduna amma abin ya citura, an kira wayarsa baya dauka, an kuma tura masa sakon kar ta kwana bai ce komai ba.