
Daga Musa Mohammed
Matan aure da ’yan mata a wasu unguwanni kamar Dorayi inda Gwamna Abba Kabir Yusuf (Abba Gida-Gida) ya fito, da wasu kauyuka na Jihar Kano na kwana a wajen rijiyoyi da fanfunan ruwa saboda ƙarancin ruwan sha da ya addabi yankin.
A unguwar Dorayi, da ke ƙaramar hukumar Gwale, al’umma na fama da matsalar ruwan sha da ta kai ga mata da yara na kwana a wajen kalolin ruwa, su na jiran layi ko jiran ruwan ya cika.
A cewar al’umma mazauna unguwar ta Dorayi, sunce, sun dade suna fama da wannan matsala ba tare da an samu mafita daga gwamnati ba.
Haka ma al’ummar dake kauyen ‘Yar Manman dake karamar hukumar Tsanyawa, sun koma so sai.
“Wannan ruwan da muke sha, dabbobi da mutane ne ke haduwa a wajen. Amma ba mu da wani zaɓi, sai mu sha shi ko da kuwa yana da haɗari,” inji wata mata da ke zaune a kauyen.
Fiye da mutane 10,000 daga kauyen da kuma wasu ƙauyuka biyar da ke kusa da shi ne ke amfani da ruwan.
A yanzu haka, wasu yara mata sun daina zuwa makaranta saboda sai sun fita neman ruwa tun da asuba, kuma su na dawowa da yamma su gaji, har ba su iya komai.
“Yanzu yara mata basa zuwa makaranta, su na ta fita neman ruwa. Ko sun dawo gajiya ce kawai,” inji wani mazaunin kauyen.
Wannan matsala na haddasa yaduwar cututtuka masu nasaba da rashin tsaftar ruwa, kamar amai da gudawa da ciwon ciki, lamarin da ke barazana ga lafiyar jama’a.
A wani bincike na masana, sun gano cewa Kano Na Bukatar Litar Ruwa akalla Miliyan 700 Domin Biyan Bukatun Yau Da Kullum, amma abinda ake samarwa bai wuce lita dubu dari biyar ba (500,000).
Yanzu dai al’ummar jihar kano zasu sa ido su gani ko gwamnati zata dauki matakin gaggawa domin shawo kan Matsalar ruwan sha da ya ta’azzara.