
Bello El-Rufai Da Usman daga zaria Road an samu munmunan sabani, akan taimako da ya nema.
Bello El-Rufai shine dan Majalisar wakilai mai wakiltar kaduna ta Arewa, sun samu sabani da Malam Usman dake Doka Kuma mazaunin Layin Zaria road a karamar hukumar kaduna ta arewa, domin ya nemi taimako yaran shi basu da lafiya yana neman kudin magani ko asibiti Bello El-Rufai bai taimaka masa ba, har yakai ga sa’insa a waya tsakanin Malam Usman da Bello.
Wata majiya kwakkwara ta bayyana wa MURYAR TALAKAWA cewa Bello El-Rufai yacewa Usman ta waya cewa shi mutane na yawan damunsa da roko suna neman taimako, kuma shi shine shugaba ba Usman ba abinda yakeso dole tsarinsa za a abi, ya kara da cewa Usman ya kirashi ba tare da izini ba, domin Layin da nashi na musamman ne wato (private line), don haka Usman yayi babban laifi da ya kirashi domin bashi ya bashi lambar ba, kuma kar yakara kawo mishi misali da lokacin kamfen wato yakin neman zabe, yace shi ba ruwanshi da wannan, wancan lokacin bai canza halinshi ba, yanzu ma ba canzawa zaiyi ba, zaiyi blocking dinshi in baiyi hankali ba, “Ni duk Wanda bani na bashi lamba ta ba, ko na bashi izini yakira ni, zanyi blocking dinshi” inji Bello El-Rufai.
Akarshe dai mun samu labari cewa anyi baran baram tsakanin Malam Usman da Bello El-Rufai.
Mutanen mazabar kaduna ta arewa inda Bello El-Rufai ke wakilta suna ta korafi cewa sunyi da nasani zaben Bello domin baya daraja mutane, baya kuma sauran mutane, sai wasu ‘yan tsirarru Wanda sune masu yi mishi fadanci, domin samun na Miya, kuma basu iya gaya mishi gaskiya, su kadai ne kawai ke zuwa inda yake ko su kirashi a waya.
Mutanen mazabar kaduna ta arewa sunce lallai ‘BAREWA BATA GUDU DANTA YAYI RARRAFE’.
“Tun ba aje ko ina ba, an fara samun matsala dashi, ya fara gasa mana aya a hannu, Jika-Hanta ya koma Gasa-Hanta”.