
Daga Kwamared Musa Mohammed
Zababben Gwamnan Jihar kaduna, Sanata Malam Uba Sani Alheri ne ga Al’ummar jihar ganin yadda ya Fara dawo da martabar jihar a idon duniya.
Ya fara dauko hanya yadda tattalin arzikin jihar zai bunkasa, kiwon Lafiya da harkar ilimi su inganta, Wanda Hakane zai sanya masu zuba Jari daga kasashen duniya su Nuna sha’awarsu wajen zuba Jarinsu a jihar kaduna.
Cikin kankanin lokaci gwamnatin jihar kaduna karkashin jagorancin Malam Uba Sani, za aci gaba da Gina da gyara asibitocin da makarantun da Gina hanyoyi, da bunkasa harkar noma da tsaron al’umma tareda dukiyar su.
Ina Mai tabbatar wa da al’ummar jihar kaduna da cewa jihar kaduna zasu ga nasarori da ci gaba Wanda ba a Taba ganin irinsa ba.
Malam Uba Sani Adalin Shugaba Ne Abun Koyi, yadda yake jajircewa wajen shugabancin al’ummar jihar, da yadda gwamnan yafara amfani da basirar sa wajen magance matsalolin jihar kaduna.
Ina mai tabbatar wa da al’ummar jihar kaduna, Malam Uba Sani zai yi amfani da hikima da kwarewar sa wajen magance halin da ake ciki a jihar kaduna.
Malam Uba Sani ya cancata a yaba Masa na yunkurin sa, a matsayin wani mataki na ganin ya hada kai da gwamnatin tarayya wajen kawo karshen matsalar Jihar kaduna.
Uba Sani ya dauko hanyar da zai yi wa al’ummarsa hidima ta hanyar da ta dace, saboda kishinsa na samun zaman lafiya.
‘Kyawun hali yafi komai mahimmanci a cikin shugabancin al’umma’.
Bahaushe yace, idan sallah ta lalace, a tuhumi limami. Babu abunda ya kai kyawun zuciya mahimmanci a wajen jagoran kowacce irin tafiya. Idan akwai hali mai kyau komai zai iya samuwa.
Tabbas, mu al’ummar jihar kaduna munyi gamon katari, munyi daven shugaba adali, mai nagarta.
Uba Sani hazikin gwamna mai tarbiya, wannan shine zai da asamu cigaban tattalin arziki, tsaro, farin ciki da son juna a cikin mutanen saboda da kyawun halinsa.
Adalin shugaba ba a ganeshi a fuska ko a kalamansa sai an dorashi akan mulki, mun gano Malam Uba Sani Adali ne tun yana Majalisar Dattijai wato matsayin Sanata mai wakiltar kaduna ta tsakiya, inda yayi wasu abubuwa da ya nuna shi adali be, bayan an zabe shi an kuma rantsar dashi a matsayin gwamnan jihar kaduna, ya nuna shi adalin shugaba ne ta hanyoyi da yawa a cikin kankanin lokaci.
Ina Kira ga al’ummar jihar kaduna da mu cigaba da baiwa gwamnatin Jihar kaduna karkashin jagorancin Malam Uba Sani goyon baya, domin asamu nasarori da ci gaba.