
Marayu Takwas Duk Mata, Aikawa Charity Foundation Ta Kai Agajin Gaggawa kamar Haka:
Gina musu sabon gida Katon gaske kuma ginin zamani.
Samar musu da katifun barci da fulalluka da gadon kwanciya da kujeru.
An saya musu kayan abinci na kusan naira dubu dari uku.
An sayawa mahaifiyarsu buhun gyada naira dubu sabain domin taci gaba da sanaar man kuli da kuli da gyada.
An baiwa mahaifiyarsu naira dubu hamsin domin tayi sanaar kayan miya da maggi da sauransu.
An sayawa “yammatan keken dinki domin koyar sanaoin dogaro da kansu.
An saya musu dukkan kayan amfanin gida.
An kai mara lafiyar asibiti mai tsada an duba uwa da “yar da uwar.





















Sune marayunnan guda takwas wadanda mahaifinsu ya rasu yabarsu su 8 dukkansu mata.
Bandakinsu ya rushe, ana hangosu daga waje.
Sannan basuda abinci ga kuncin rayuwa.
Tabbas yau sun sami farin ciki da jin dadi
Da yawansu har kukan murna sukayi saboda jin dadi.
Allah ya sakawa wadanda suka taimaka da alheri ya farantawa rayuwarku.
Allah ya kara mana lafiya.
SANI ROGO AIKAWA.
CEO AIKAWA CHARITY FOUNDATION.
08082744019 WATHAAP.
08103555058