
Masu anfani da taliyar Indomie a Nijeriya ya kamata su sani cewa, anan gida Nijeriya ake yin taliyar Indomie ba daga waje ake shigowa da ita ba, ba ya dauke da wani sanadari mai hadari ko cutarwa.
Tunda taliya na cikin haramtattun Kaya da aka hana shigowa dasu cikin gida Nijeriya, Hukumar NAFDAC tayi Kira ga masu anfani da ita, da su rinka sayan Wanda akayi anan gida Nijeriya.
Bugu da Kari, duk lokacin da aka tayar da magana akan illar yawan cin taliya Wato ‘noodles’ a sassa na duniya, sai afara jingina matsalar da taliyar Indomie da ake Yi anan Nijeriya.
Azahirin gaskiya duk bai wuce karbuwa da taliyar Indomie ta samu ne ba.
“Bugu da kari ta samu karbuwa ga al’ummar Nijeriya da ma sauran kasashen duniya”Ta tserewa sauran kamfanoni masu sarrafa taliya a Nijeriya da duniya baki daya wurin karbuwa ga masu amfani da ita, hakan ya samo asaline na sarrafa taliya Indomie mai Inganci Wanda kowa yakeso yayi amfani da ita.
A shekarar 2022, akwai bayani da aka wallafa a yanar gizo wato ‘online’ daga ‘Yan kasuwa ko masu cinikaiya a Afirka ta gabas da Afirka ta kudu, a kasar Misira wato Egypt, ana gargadin mutanen kasar da su guji amfani da taliyar Indomie kowace irice aaboda rade-radin iya kamuwa da wani cuta saboda sanadari dake cikin taliyar.
Haka aka ta yada jita-jita a kasashen Larabawa da suke makwabta da kasar Egypt, abin ya watsu.A nijeriya, kafafen yada Labarai sunyi anfani da jita-jita da akeyi akan sanadari mai hadari acikin taliyar Indomie Wanda ya samo asali daga Egypt, a inda abin ya kawo tarnaki ta rashin tashina har yakai ga Hukumar kula da Inganci abinci da kayan masa rufi wato NAFDAC da Kuma Hukumar kula da Inganci kayayyaki wato SON sukayi binckike na musamman suka Kuma tabbatar cewa ‘Yan Fasa Kwauri ba su shigo da gurbataccen taliyar Indomie cikin gida Nijeriya ba.
A karshen bincike da aka gudanar, anfani cewa Babu wata hanya da aka samu ta shigowa da taliyar da aka haramta shigowa ta ita, Kuma har a kasuwanin mu Babu irinta, ansamu tsaro sosai.
Jita-jita da ya madidi da ake tayi game da sanadari na ethylene da oxide, Wanda akace yana haifar da ciwon daji (cancer) Wanda aka gano ana anfani dashi wurin sarrafa taliyar Indomie kamar sanadarin chiken flavour a kasar Taiwan da kasar Malaysia Wanda akace kwararru akan harkar Ingancin lafiya a kasashen guda biyu suka tayar da balli akan sanadarin da suke cewa wai yana haifar da cancer Wanda ya kawo tarnaki akan taliyar Indomie da ake sarrafa was a nan gida Nijeriya.
Kafafen yada Labarai sune ummul-abai’sin yada labarin kanzo kurege suna fadin abinda ba haka yake ba.
Indofood sune suke sarrafa taliyar Indomie akasar Taiwan da Malaysia, sa Annan kuma Dufil Prima Food Plc a Nijeriya sune suke sarrafa taliyar Indomie (Instant Noodles) Wanda suke fuskantar kalu bale.
Amma kuma wasu kafafen yada Labarai sun ruwaito cewa dalilin Hana shigowa da taliyar kwanan na ne a dalilin cece kuce da akeyi akan sanadarin da ke cikin taliyar mai haifar da cancer, amma maganar gaskiya shine an hana shigowa da taliyar Indomie daga waje ne shekaru masu yawa domin masu masana’antun mu da kayansu su samu karbuwaa gida Nijeriya da Kuma kara musu kwarin gwuiwa domin Kar su durkushe.Shugaban Hukumar kula da abinci Inganci kayayyakin masarufi wato NAFDAC, Mojisola Adeyeye,yace taliyar “Instant noodles” na cikin jerin sunayen abubuwan da Gwamnatin Tarayya ta Hana shigowa dasu nijeriya.
Shi wannan sanadari da ake magana, bayi da rajista da Hukumar NAFDAC Kuma ba Nijeriya ake sarrafa Shiba.
Hana shigowa da taliyar ‘instant noodles’ dadadden al’amari ne, “Hukumar NAFDAC ta dukufa wurin gwaji da tantance taliyar Indomie da kuma sanadarin da ake amfani dashi, har da shiga cikin kasuwanin mu domin su tabbatar ba shigo da haramtacciyar taliyar ba ta barauniyar hanya cikin Nijeriya.
Acewar Hukumar NAFDAC, “abinda mukeyi shine tabbatar da cewa ba ba a shigo da taliyar ba ta haramtacciyar hanya, in Kuma har an shigo dashi, muna da jami’ai masu kwazo da zasu gano haka.Muna so Kuma mu tabbatar cewa duk sanadarin da ake amfani dashi wurin yin taliya a Nijeriya an gwada su an tabbatar Basu da illa ga lafiyar masu cinsa.
Saboda haka, Hukumar NAFDAC bata hana sarrafa, ci ko sayar da taliyar Indomie ba, “tace Babban manaja Kuna Jami’in Hulda da jama’a na kanfanin Dufil Prima Foods Plc, Tope Ashiwaju, yace, munaso mu tabbatar was da manyan kwastamomin mu a Nijeriya cewa duk taliyar Indomie da muke sarrafawa a nan tana tsaro da Inganci tare da sahalewar hukuma Mai kula da Inganci kayayyakin masarufi ta duniya wato (ISO).
Saboda haka, muna bin kaida wurin sarrafa taliyar Indomie a duk kamfanonin mu dake fadin kasarnan Nijeriya, ” mu masu bin dokokin Hukumar NAFDAC ne, da Hukumar SON a duk harkokinmu ko da yaushe, duk taliyar mu tana dauke da sanadari masu Inganci, sa’anan Kuma, Hukumar NAFDAC da SON sun tantance kayanmu, sun tabbatar babu wani sanadari mai cutarwa”.