
Daga Kwamared Musa Mohammed
Alhaji Lawal Samaila Yakawada, Tsohon sakataren gwamnatin jihar kaduna, jigo a jam’iyyar APC, ya taya zababben gwamnan Jihar kaduna, Sanata Uba Sani, da mataimakiyansa, Hajiya Hadiza Balarabe Sabuwa, murnar nasarar da suka samu a zaben Gwamna na ranar Asabar.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da ya baiwa Yan jarida a kaduna.
Nasarar Uba Sani Ta Tabbatar Da Dimokuradiyya Na Raye A Jihar kaduna da Kuma Nijeriya.
Yakawada ya kuma yabawa magoya bayan jam’iyyar da suka bayar da ruwan kuri’unsu ga ‘yan takarar jam’iyyar APC jihar kaduna.
Yayi Kira ga daukacin Al’ummar jihar kaduna da su marawa sabuwar gwamnatin karkashin jagorancin Sanata Uba Sani, domin ciyar da jihar gaba.