
Daga Kwamared Musa Mohammed
Hon. Abubakar Mahmoud ‘Jarma’ ya taya zababben Gwamnan jihar kaduna, Sanata Uba Sani murnar lashe zaben bana na 2023, Jarma ya ce, Al’ummar jihar kaduna sun yi zabin da ya dace, wanda zai kai su ga ganin ci gaba nan ba da jimawa ba.
Ana ci gaba da aika sakon taya murna ga Sanata Uba Sani tun bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe a bana.Da yake taya Uba Sani murna a zantawar da da manema Labarai ranar Lahadi a kaduna, Jarma yace zaben APC da Uba Sani alama ce ta fata na gari ga mutanen jihar kaduna.
A cewarsa: “UBA SANI da HADIZA SABUWA ne gamin da ya dace da jihar kaduna a wannan lokacin. “Al’ummar jihar kaduna sun yi magana da babbar murya da fata mai kyau ga jihar ta hanyar zaban Uba Sani/Hadiza”.
“Uba Sani nagartaccen dan siyasa ne, gogewarsa a siyasa babu shakka zai yi amfani da ita wajen sauya fasalin jihar kaduna. “Ina kira ga dukkan ‘yan jihar kaduna da mazauna ciki har da ‘yan takarar da suka yi takara tare dashi da su marawa shugabancin zababben Gwamna wajen ginawa da hada kan jihar kaduna ta ci gaba.”
