KUJERAR GWAMNA A KADUNA 2023: BABU KWARARRE KUMA GOGAGGEN DA ZAI IYA TAKA RAWAR GANI KAMAR SANATA UBA SANI – KWAMARED MUSA MOHAMMED

‘Kujerar Gwamna A Kaduna 2023: Babu Kwararre Kuma Gogaggen Da Zai Iya Taka Rawar Gani Kamar Sanata Uba Sani’

Duk masu neman gujerar Gwamna a kaduna, babu kwararre kuma gogaggen da zai iya taka rawar gani kamar SANATA UBA SANI, domin Kwarewar sa a matsayin mai taimaka wa shugaban kasa a lokacin gwamnatin Obasanjo, mashawarcin Gwamnan jihar kaduna Nasiru El-Rufai kan harkokin siyasa da kuma tarihin sa a majalisar dattawa a inda yayi abubuwan da bawani sanata a jihar kaduna yayi irinsa.
Ba girman kujerar muke dubawa ba, muna la’akari da dan siyasar da zai iya taka rawar gani wajen kawo cigaba, hadin kai ga jam’iyyar APC a jihar kaduna.

Uba Sani yana da sanayya da hanyoyin da zai bi wajen samarwa jihar kaduna kudadeen shiga da zai baiwa gwamnanati damar cigaba da ayyukan da ta sanya a gaba.
ya zama wajibi al’ummar jihar kaduna su yi kokarin ganin APC ta samu nasara a zaben 2023.
Don haka ina kalubalanci ‘yan jam’iyyar APC na jihar kaduna da su rubanya kokarinsu kafin shekarar 2023.
Mu kuma cigaba da baiwa Sanata Uba Sani da jam’iyar APC goyon baya domin samun nasara a zabe Mai zuwa 2023.

Leave a comment

Design a site like this with WordPress.com
Get started