2023: ‘Bello El-Rufai shine zabin mu’ – Kwamared Musa Mohammed

Bello El-Rufai shine zabin mu’

Dukkan masu neman wannan matsayin na wakili a Majalisar tarayya babu kwararre kuma gogaggen da zai iya taka rawar gani kamar Hon. Bello El-Rufai, domin ya nuna cewar yana da kwarewar da zai rike wannan matsayin idan jam’iyyar al’ummar karamar Hukumar kaduna ta Arewa in aka ba shi dama. ‘Bello El-Rufai shine zabin.mu’

Yanzu lokaci ne na matasa, kuma lokaci ne da ya kamata a zaɓi mutumin da yake da kishin kawo cigaba wa yankin sa.

“A yayin da zaben shekarar 2023 ke karatowa al’ummar karamar Hukumar kaduna ta Arewa masu kada kuri`a su shiga taitayinsu, saboda zababben wakilin a Majalisar tarayya Hon. Samaila Suleiman ya shiga rigar alfarma, amma da ya samu nasara ya watsawa masu zaben kasa a ido”.Mu magoya bayan APC da Hon. Bello El-Rufai Dan takarar kujerar Majalisar tarayya a karamar hukumar kaduna ta Arewa karamar hukumar muna neman alfarmar mutane musamman idan an zo zabe a 2023 dasu zabi BELLO ELRUFAI domin za a samu wakilci nagari, saboda muna da tabbacin da samar da wakilci mai inganci.
“Yanzu mu a karamar Hukumar kaduna ta Arewa muna bukatar matashi haziki irin Bello El-Rufai”.

Design a site like this with WordPress.com
Get started