
Masani a harkar siyasa Kuma mamba a jam’iyar APC a jihar kaduna Kwamared Musa Mohammed ya bayyana nagartar Bello El-Rufai Dan takarar kujerar Majalisar kaduna ta Arewa ta fuskoki da dama wanda yake ganin shi ne mafi cancanta wakilci al’umma.
Yayin da yake tattaunawa da manema labari ranar Alhamis a kaduna game da wanda zai zama jagora kuma wakilin al’ummar kaduna ta Arewa a Majalisar tarayya na gaba a 2023, masanin ya bayyana Bello El-Rufai a matsayin dan takarar da yafi nagarta acikin sauran Yan takaran.
“Bello El-Rufai shi ya cancanci ya zama wakilin al’ummar kaduna ta Arewa a 2023”
Kwamared Musa ya bayyana cancanta, hazaka, Nagarta, sanin yakamata na Malam Bello El-Rufai matsayin muhimman abubuwan da za su sa a zabi shi a matsayin wakilin al’ummar kaduna ta Arewa.
“Ina Kira ga al’ummar kaduna ta Arewa da su zabi MALAM BELLO EL-RUFAI a matsayin dan Majalisar wakilai da zai wakilce mu domin samun wakilci nagari”.
